TF RiverS - шаблон joomla Окна
Please select your page

Kassu Zurmi Da Wakokinsa

Author(s): Ahmad Magaji
Created by: Super User

Marigayi kassu Zurmi, daga Zurmi a Jihar Zamfara, Najeriya, wanda sunansa na yanka shi ne Abubakar, ya shahara mutuka akan kidan farauta, wakar ‘yan tauri da kuma wakokin barayi. Watua a takaice, kassu Zurmi makadin maza ne shi.Farauta tsohuwar sana’a ce ta neman abinci ga dan Adam, musamman maa dai a kasar Hausa. Tun zamani mai tsawo Hausawa kan yi shiri su fita dun su kamo naman daji, wadanda kuwa hadari gare su.

Akan ci karo a dajin da dabbobi iri-iri ,kamar su bauna, damisa da kyarkeci; wani lokaci ma har da zaki ko giwa . Wannan shi ya sa duk mai niyyar shiga farauta sai ya shirya sosai,ya nemi magungunan kariyar kai, irin su maganin karfe da na gora da kua-da-bara; watau dai ya zama cikakken dan tauri.

To, tun da makadin masu farautar yakan kasance tare da su duk inda suka shiga, wannan ya sa shi ma dole sai ya zama namijin gaske. Ta haka ne Kassu Zurmi ya yi suna ainu, wajen tsara wakokin da sukan tsima maza a daji, su zabura su ja daga da kowace irin dabbar da za su hadu da ita. Allah ya ba shi basira mai yawa ta wannan fannin, inda yakan yi amfani da kalmomi masu kyau, wadanda ba kasafai akan ji wasun su ba a lafazin Magana ta yau-da-kullum, idan ba wajen masu sana’ar farautar ba. Allah kadai Ya san yawan irin wadannan wakokin da Kassu Zurmi ya shirya a lokacin rayuwarsa.

Wannan littafin mai suna Kassu Zurmi da Wakokinsa, jagora ne ga masu nazari a fannoni da yawa, musamman ma wadanda suka danganci rayuwar shi kansa mawakin, da sana’ar farauta a kasar Hausa, da harkar adabin gargajiya a harshaen Hausa.

Doktan Ahmad Magaji, babban malami ne a Sashen Koyar da Haursunan Nijerya na Jamil’ar da ke Kano. Ya gudanar da ayyukan bincike da dama akan nazarin adabin Hausa. Hasali ma, asalin wannan littafin kundin bincike ne wanda ya gabatar a cikamakin karatun digirinsa na farko a shekarar 1980; daga baya ne ya bunkasa shit a hanyar kara yin bincike mai zurfi.

Dokta Ahmad Magaji ya yi rubuce-rubuce da dana, wadanda suka hada da shahararren littafin nan na tarihin rayuwar marigayi sheikh Abubakar Mahmud Gumi mai suna Manufaata wanda suka fassara tare da marubucin littafin na farko cikin harshen Turanci, watau Farfesa Isma’ila A. Tsiga, na Sashen Koyar da Turanci da Nazarin Adabi a Jami’ar Bayero ta Kano, Najeriya.

Ask about this product

Comments

Buy now

You can now buy this awesome Joomla Theme directly on Themeforest for a really low price for this awesome and stunning Joomla product!

Nulla vitae elit libero, a pharetra augue. Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Etiam porta sem malesuada magna mollis euismod. Morbi leo risus, porta ac consectetur ac, vestibulum at eros. Nulla vitae elit libero, a pharetra augue.


BUY ON THEMEFOREST

×

Login

Please login using your credentials recived by email when you register.

  or   Create an account

Forgot your password? |  Forgot your username?

×

Register now


I'm a small Introtext for the Register Module, I can be set in the Backend of the Joomla WS-Register Module.  or   Login
×